Wasu masu kishin addini a Sokoto sun bukaci a gaggauta sakin wadanda ake zargi da hannu a kisan da aka yi wa Deborah Yakubu, ɗaliba ƴar aji 2 a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari.

Masu zanga-zangar da suka yi tsinke a fadar Sarkin Musulmi a yau Asabar, sun bukaci a gaggauta sakin ƴan uwansu, wadanda a ke zargi da kisan dalibar a bisa zargin furta kalaman ɓatanci ga. Annabi Muhammad (SAW).

Masu zanga-zangar na dauke da kwalaye da ke dauke da rubuce-rubuce kamar su“Ku saki ƴan’uwanmu,” “Musulmi ba ƴan ta’adda ba ne,” a gaban jami’an tsaro.

Ana zargin wani Malami mai suna Isiyk ne ya shirya zanga-zangar, wanda ya yi imanin cewa wadanda ake zargi da kisan sun kare mutuncin Annabi Muhammad (SAW) ne.

“Assalamu alaikum, muna kira ga daukacin al’ummar musulmin jihar Sokoto da su fito zanga-zanga saboda ‘yan uwanmu da aka kama wajen kare addininmu – Musulunci. Wadanda suke daukaka darajar annabinmu SAW,” in ji sakon zanga-zangar da Malamin ya raba wa musulmin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here