Masu son kafa ƙasar Oduduwa na zanga-zanga a Osun
Masu son kafa ƙasar Oduduwa a yankin ƙabilar Yarbawa kudu maso yammacin Najeriya sun haɗa gangami a garin Osogbo babban birnin jihar Osun.
Sun fito zanga-zanga duk da gargaɗi da aka yi su ƙauracewa zanga-zangar.
Jaridun kudancin Najeriya sun wallafa hotuna da bidiyon masu zanga-zangar a kafofin sadarwa na intanet.
An nuna masu zanga-zangar riƙe da tuta da kuma kwalaye da ke bayyana da’awarsu ta kafa ƙasar Oduduwa mai cin gashin kai.
Jaridar The Nation ta wallafa bidiyon masu zanga-zangar na rera take.
Rahotanni sun ce an baza jami’an tsaro a dandalin Nelson Mandela a Osogbo, inda yawanci masu fafutikar ke haɗuwa.