Masu sayar da shinkafa ‘yar gida suna so Buhari ya kama masu sayar da shinkafar waje

BBC

Kungiyar manoman shinaka ta Najeriya ta nemin gwamnatin tarayyar kasar ta rika kama masu sayar da shinkafar waje.

Kamfanin dillancin labarai na kasar NAN ya ruwaito cewa, shugaban kungiyar Mista Andy Ekwelem ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja babban birnin tarayyar kasar.

Kungiyar ta yi wani taron manema labari ne domin ta nuna karuwar matsalar shigo da shinkafar waje cikin kasar wadda aka haramta.

Shugaban ya kuma ja hankalin gwamnati kan cewa matukar ba a dauki tsattsauran mataki kan masu shigo da shinkafar ba, to kuwa masana’antun da suke samar da ita a cikin gida za su durkushe.

Ekwelem ya ce tun bayan lokacin da gwamnatin tarayya ta bude kan iyakokinta, shinkafar ketare ta cika kasuwa makil.

“Mun sha fadin cewa ya kamata gwamnati ta rika kama masu shigo da shinkafa da kuma masu manyan kantina na zamani. Shin kafa ce kan gaba a abubuwan da babban bankin Najeriya ya haramta shigo da su,” in ji Ekwelem.

Ya kuma ce gabanin zuwan shugaba Buhari a 2015, kwamfanonin samar da shinkafa da ake da su ba su fi shida ba, amma a yanzu akwai kimanin 60.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here