Masu katin ƴan ƙasa za su biya kuɗi idan suna son gyara wasu bayanai – NIMC

NIN

Hukumar Samar da Katin Ƴan Ƙasa ta Najeriya NIMC, ta ce ƴan ƙasar da ke da lambar katin ƴan ƙasa ta NIN za su dinga biyan wasu kuɗaɗe a lokacin da suke son sauya bayanansu ko sauya katinsu na ƴan ƙasa.

Wani babban jami’i a hukumar Funmi Opesanwo, ta ce kuɗaɗen da za a dinga cajin mutanen na yin wasu sauye-sauye ne.

Ta ce suna da tsare-tsaren ayyuka daban-daban da hukumar ta tanadar kamar idan mutum na son sauya suna ko adireshi ko kuma sauya katin, inda a nan ne za a biya wasu kuɗaɗe, amma idan mutum zai yi rijista ne a karon farko to ba zai biya komai ba.

Ga mutanen da ke son sauya ranar haihuwarsu, za su biya naira 15,000.

Idan kuma adireshinka za ka sauya ko kuma za ka gyara sunanka, to naira 500 kacal za ka biya.

Idan kuma sauya katinka za ka yi da sabo to za ka biya naira 5,000.

Madam Opesanwo ta ce: “Domin saua ranar haihuwa, kudin da za a biya N15,000. Idan kuma sauya kati za a yi, to za a biya N5,000. Domin gyara adireshi ku suna kuwa, abin da za a biya N500. Don haka mutane ba su fahimci abin ba, sai suka zaci NIMC ta ce su biya wasu kuɗaɗe ne. Wannan kuɗi na sauye-sauyen da mutum ke so ne.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here