MASU GARKUWA DA MUTANE,NE SUKA ƘONA MAHAIFIYARTA DA WUTA, SUKA BANI ITA INSHAYAR DA ITA.

Wata mata, Safara’u Falalu da ta tsira daga Hannun masu garkuwa da mutane, ta sheda wa Jaridar Katsina City News haka a zantawar su da wakilin mu, a birnin katsina.

Safara’u tace: “masu garkuwa da mutanen sun taremu ne a ƙauyen mai yaɗiya dake ƙaramar hukumar Funtua Inda suka buɗe wuta suka kashe Direba da wata mata, mu kuma da Uwar wan’nan yarinyar da sauran fasinjojin motar suka tafi damu cikin Daji sukai ta gana mana azaba, har suka kashe uwar yarinyar nan dake hannuna, suka ƙonata da wuta sai suka kirani suka bani yarinyar sukace Inbata Nono, nacemasu bani da Nono, sukace incire rigata nacire suka kamamin Nono suka matse har ya kwalje, na suma bansan inda kaina yake ba, bayan na falko sukece lallai sai nabata Nono. Ahaka dai nake bata ba kuma don akwai ruwan Nonon da yarinyar zata iya sha wadatacce ba ba. Saida muka kwana bakwai a hannun su Allah ya kuɓutar dani da wani malami da yaketa karatun Al’ƙur,ani’ sukace ya ishesu hakanan zasu sallameshi yatafi gida, sai yacemasu ni ɗiyar sa ce, sai suka ɗauko mu busa mashin da ita jaririyar sukaita gudu damu da bindigu a tare dasu har asuba sanan suka ajemu kusa da hanya alokacin ni ko tafiya ma bani iya yi. Muka samu wasu bayin Allah suka taimaka suka kaimu wani ƙauye a kusa da Zariya, anan muka samu motar da takawo mu gida, shi malamin sun ajeshi a Dutsinma, ina tunanin ɗan can ne. Yanzu ni Allah ya kuɓutar dani da wan’nan jaririyar da bansan kowa nata ba, gata dai a hannuna idan darabo Allah ya rayata Allah ya albarkace ta”

Damuka tambayeta game da Abinci, Safara’u ta sheda mana cewa ana basu ɗanyen Dankali da ruwan fiyawata guda ɗaya susha su biyu ita da malamin da bata ambata mana sunan sa ba, kuma su rage, idan jaririyar tayi kashi ta wanke mata da ragowar ruwan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here