Advert
Home Sashen Hausa Masu Garkuwa Da Mutane Sunyi Garkuwa Da Kanwar Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin...

Masu Garkuwa Da Mutane Sunyi Garkuwa Da Kanwar Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina

 

Daga Ibrahim Da’u Mutuwa Dole

Anyi garkuwa da kanwar mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Katsina Shehu Dalhatu Tafoki, Mai suna Asma’u Dalhatu tafoki.

‘Yan bindigar sun kai hari kauyen Tafoki da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina inda suka yi garkuwa da wasu mutane.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga Aminiya, dan majalisar ya ce, “Eh, gaskiya ne‘ yan bindiga sun sace kanwata, Asma’u Dalhatu a safiyar ranar Lahadi.

“Sun kutsa cikin garin da misalin karfe 1am sannan suka nufi gidan shugaban kauyen, wanda shine gidan dangin mu kuma suka sace‘ yan uwan ​​mu mata biyu.

“A kan hanyarsu ta zuwa dajin, sun ci karo da wasu‘ yan kungiyar ’yan banga kuma sun yi musayar wuta. Ana cikin haka sai daya daga cikin ‘yan matan ta tsere ta koma gida, amma dayar ba ta iya guduwa, don haka suka tafi da ita,” inji shi.

Tafoki ya ce masu garkuwar ba su nemi wata bukata ta neman kudin fansa ba.

Lamarin ya faru ne jim kadan bayan ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Kurami da ke karamar hukumar Bakori a jihar, inda suka sace mata da‘ ya’yan Dr Ibrahim Kurami, wanda kuma dan majalisar Katsina ne.

Daily Trust

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: