Ɓarayi ƴan bindiga sun yi garkuwa da wata mata da miji da ƴaƴan ta 2 a katsina.
@Katsina city news.
A daren jiya talata wajen misalin ƙarfe 2 na dare wasu masu garkuwa da mutane suka dira a unguwar Sabon gida dake cikin Birnin katsina, Agidan wata mata maisuna Hajiya Rayya bayan ɗaukar sama da sa’a ɗaya suna ɓalle gate ɗin gidan, suka shiga sukayi awon gaba da matar da mijinta da ƴaƴanta 2 daga bisani kuma sun sako mijin da ƴaƴan biyu suka tafi da matar bayan sun amshi lambar wayar babban ɗan nata danufin zasu nemeshi.
Yazuwa yanzu dai babu wani tabbacin halin da matar take ciki ko kuma neman wani kudi domin sakota.