Wasu gungun masu Garkuwa da Mutane da suka rasa hanyar da zasu fitar da Kansu bayan yin Garkuwa da wata mata da diyarta, sun sheka barzahu bayan kwallin kura da jami’an Yan Sanda a Karamar Hukumar Kafur ta Jihar Katsina.

Kakakin Rundunar S.P Gambo Isah ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Hedikwatar Rundunar da ke Katsina.

A cewar Gambo Isah, masu Garkuwa da mutanen sun shiga wani Kauye Mai suna Gamzako inda suka yi awon gaba da wata mata Mai suna Hama Sanusi da diyarta Aisha Sanusi, sai dai sun bace hanyar su ta ficewa daga kauyen.

Bayan sun tambayi wasu mutanen garin ne akan su nuna masu hanya aka gane cewa Yan ta’adda ne, inda nan take aka sanar da Yan sanda kuma suka yi musayar wuta da su wanda hakan ya bada damar hallaka Yan ta’addan biyu.

Bayan hallaka Yan ta’addan, an samu bindiga Kirar AK 47 guda daya da harsasai guda 4, gami da karamar bindiga (Pistol) guda biyu da harsashin ta na turawa guda 6 sai layoyin su da sauran kayan tsafe-tsafe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here