Masari Ya Yaba Wa Dikkko Bisa Bada Tallfi Ga Yayan Jam’iyar APC.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya yaba wa Dr. Dikko Umar Radda bisa yadda yake samar da muhimman kayayyakin ga jami’an jam’iyar APC dake kananan hukumomin Batagarawa, da Charanchi da kuma Rimi.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin siyasa Kabir Shu’aibu Charanchi, ya yi yabon ne a wurin rabon kayayyakin a garin Rimi.

Gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar Katsina da su zabi ‘yan takarar jam’iyyar APC a zaben kananan hukumomin jihar Katsina dake tafe.

A nasa jawabin shugaban hukumar dake kula da kanana da matsakaitan sana’o’i na Najeriya (SMEDAN) Dr. Dikko Umar Radda ya tunatar da ‘ya’yan jam’iyyar APC da su bada goyan a dukkan matakai.

Dikko Radda wanda ke neman kujerar Gwamnan Jihar Katsina a zabe mai zuwa, ya yi nuni da cewa ya kamata jami’an jam’iyyar APC da duk masu ruwa da tsaki su zagaya a kowane lungu da sako na jihar nan don wayar da kan jama’a akan bukatar zaben ‘yan takarar jam’iyyar APC a zaben karamar hukumar dake tafe.

Kayayyakin da aka raba sun hada da mota daya daya ga daukacin shugabannin jam’iyyar APC na kananan hukumomin Batagarawa, da Charanchi da Rimi, da babura guda 100 ga shugabannin uku, da naira dubu goma ga wasu zababbun matasan mazabu 3.

Sauran kayayyakin da aka raba sun hada da shinkafa, da masara, da gero ga ‘yan jam’iyyar domin gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki.

Taron dai ya samu halartar kwamishinan ilimi Badamasi Lawal Charanchi, da mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina Bala Abubakar Musawa, da shugaban KASROMA Injiniya Sirajo Yazid Abukur, da tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Katsina Alhaji Biyaminu Muhammad Rimi, da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here