Gwamna Aminu Bello Masari ya nemi kasar Koriya ta Kudu da ta shigo cikin hidimar aikin gona da koya sana’o’i domin bunkasa tattalin arzikin jihar da samar da ayyukan yi da sana’o’i na dogaro da kai ga al’umma musamman Matasa.

Gwamnan gabatar da wannan sakon ne a yayin da amshi bakuncin Jakadan Kasar a Najeriya, Ambasada Kim Young Chae a gidan Gwamnatin Jiha dake Abuja.

Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa, yin hakan zai habaka tare da inganta amfanin gonar da ake samu wanda zai daga darajar noman daga naci zuwa na kasuwanci. Samun hanyoyi da Injunan noma na zamani daga kasar ta Koriya zai taimaka kwarai wajan cimma wannan manufa.

A karshe, Gwamna Masari ya mika goron gayya ga Jakada Chae domin ya kawo ziyara jihar Katsina domin gane ma idon shi irin albarkar kasa da muke da domin samun kwarin guiwar amsa kiran da yayi tun da farko.

Tun farko a nashi jawabin, Mista Chae ya jaddada bukatar dake akwai ta Gwamnati ta rika tallafawa Manoma ta kowace domin harkar ta dore kuma kasar ta iya ci da kanta.

Ya kuma bayyana cewa, kasar su tana da iri na musamman wanda suka hada da na shinkafa, masara, Rogo da sauran su wadanda za a iya nomawa a Najeriya. Suna kuma da motoci da injunan Noma a farashi mai rangwame.

A nashi tsokacin, Shugaban Hukumar bunƙasa ƙanana da matsakaitan sana”o’i a Nijeriya wato Smedan Dokta Dikko Umaru Radda yayi kira ga Jakadan da su rika shirya ma jami’an Gwamnati irin shire shiren da suke shirya wa ma’aikatan hukumar tashi domin samun sabbin dubarun noman da kuma koyon sana’o’i.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here