Gwamnatin jihar Katsina, karkashin jagorancin gwamna Alhaji Aminu Bello Masari ta kashe zunzurutun kudi har naira miliyan dari ukku da sittin da takwas domin inganta kazon Ma’aikatan Jihar Katsina, su dubu ukku da dari hudu dake ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar Katsina.

Shugaban ma’aikatan jihar Katsina, Alhaji Idris Usman Tune ya bayyana hakan, a wani taron horas da daraktocin ma’aikatu da sassan gwamnatin jihar Katsina, akan fasahar Zamani, a Makarantar Koya duburun na’ura mai Kwakwalwa da yanar gizo dake cikin garin Katsina.

Alhaji Idris Tune ya ci gaba da cewa duk da jihar Katsina na fama da karancin kudi, amma ana ci gaba da horas da maaikatan jihar. Ana horas da daraktocin don ganin sun samu kwarewa akan fasahar Zamani yadda za su gudanar aikin a matsayin su na masu sanya ido kuma zama jakadu nagari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here