Gwamnan jihar Katsina ya kai ziyarar ta’aziyya a Kaita bisa rasuwar Sarkin Sullubawan Katsina hakimin Kaita Alhaji Abdulkarim Kabir Usman.

A lokacin da ya isa gidan mamacin, gwamna Aminu Bello Masari ya sama tarba daga Dan Madamin Katsina hakimin Daddara Alhaji Usman Usman Nagogo, da kuma Majidadin Katsina hakimin Tsagero Alhaji Garba Usman.

Sauran sun hada manyan yayan mamacin Galadiman Yandaki Yazid Abdulkarim, da kuma magajin garin Kaita Ibrahim Abdulkarim.

Gwamnan dai ya samu rakiyar mataimakinshi Mannir Yakubu, da kuma sakataren gwamnatin jihar Katsina Mustapha Muhammad Inwa.

Sun kuma roki Allah SWA ya gafarta ma mamacin, tare da ba iyalanshi hakurin jure rashin.

Allah ya yi ma Sarkin Sullubawan Katsina dai rasuwa ranar Juma’ar nan, kuma ya rasu yana da shekaru 68 a duniya bayan fama da jinya a asibitin kwararru dake nan Katsina.

Ya rasu ya bar matan aure 2, da yaya 37, da kuma jikoki da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here