Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya kafa sabuwar doka ta ya zama wajibi ga duk wani mai motar haya da ya fente motarsa da wani kalar fentin da gwamnati za ta samar nan gaba kaɗan. Dokar za ta fara aiki daga ranar 15 Ga Watan nan da muke ciki na wannan shekarar.

Babban Daraktan Yada Labarai Na gwamna Masari, Abdu Labaran Malumfashi ya bayyana haka ga manema labarai a gidan gwamnati jihar Katsina a yau Juma’a.

Labaran Malumfashi ya kara da cewa duk da har zuwa yanzu ba’a samar da fentin ba, amma Hukumar Kula Da Lafiyar Motaci Ta Jihar Katsina (KT VIO) za su samar da fentin, amma ya zama wajibi ga duk wani mai motar haya a Katsina ya yi wannan fenti kafin nan da 15/09/2021. Duk wanda ke da motar haya bai yi wannan fenti ba, doka za ta hau kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here