A Kokarinsa na farfado da kara wa matasa, masu fasahar Kere-keren motoci, gwamna Masari ya gabatar da wasu zakakuran matasa yan asalin jihar Katsina ga Shugaban Cibiyar Bunkasa Fasahar Kera Motoci Ta Kasa, Alhaji Jelani Aliyu a Helkwatar Hukumar Dake Abuja yau Laraba.

An zabo Matasan ne Sakamakon wata gasa da aka shirya a jihar Katsina, ta nuna irin baiwar da Allah ya baiwa matasan, wanda cikin su ne aka fitar da su saboda ƙwazon da suka nuna.

A lokacin da yake jawabi, Gwamna Masari ya ce Gwamnatin Jihar Katsina za ta yi hadin gwiwa da hukumar don ganin matasan jihar Katsina sun samu ingantaccen horo da gogewa a wannan fannin na Kere-keren motoci. Kuma ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta kara yin azama wajen yin dokokin da za su sanya a dunga sayen motocin da aka kera a Najeriya.

Da yake na shi jawabi, Shugaban Hukumar ya bayyana jin dadinsa bisa ga wannan ziyara ya kuma sha alwashin ci gaba da baiwa wadannan matasa duk shawarar da ta dace don ganin hakar su ta cinma ruwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here