Advert
Home Sashen Hausa Masari Ya Dauki Nauyin Biyan Kudin Magani Sama Da Naira Miliyan 5

Masari Ya Dauki Nauyin Biyan Kudin Magani Sama Da Naira Miliyan 5

Hon Sani Aliyu Danlami a wajen biyan kudin majinyata

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari,ya biya kudin magani kusan naira miliyan 6 ga wadanda harin yan bindiga ya ritsa da su a wasu Kananan Hukumomin Jihar.

Kwamishinan Harkokin Wasanni Da Walwalar Jama’a na Jihar Alhaji Sani Aliyu Danlami ne ya biya kudaden ga Hukumar Asibitin Kwararru ta Katsina a madadin Gwamnan.

Wadanda aka biyawa kudin maganin sun samu raunuka ne a lokacinda yan bindiga suka hari garuruwansu.

Kamar yadda Kwamishina Sani Aliyu Danlami ya shaidawa kafafen yada labarai ,wadanda lamarin ya shafa su 27 sun fito ne daga Kananan Hukumomin Sabuwa da Jibia da Dandume da dai sauransu.

Alhaji Sani Aliyu Danlami ya kara da cewar ko a kwanannan saida Gwamnatin ta biya kudin magani ga wadanda harin yan bindiga ya shafa a garin Mazoji da Batsari baya ga tallafawa iyalan wadanda suka rasu sakamakon hare-haren.

Yace Gwamna Aminu Bello Masari ya kuma samar da kayan abinci ga wadanda harin ya shafa domin saukaka masu a lokacin jinyar.

Kwamishinan ya bukaci Jama’a akan su kara jajircewa wurin addu’oi akan Allah ya kawo karshen matsalar tsaro a Jihar.

Wasu daga cikin iyalan wadanda harin ya ritsa da su sun godewa Gwamna Masari akan wannan dauki da ya kawo masu.

Sun kuma yabawa Kwamishina Danlami akan kulawa ta musamman da ya bayar ga marasa lafiyar.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...