Masari Ya Dage Dokar Hana Karin Girman Ma’aikata Da Ya Sanya A Watannin Baya A Jihar Katsina

Gwamnan Jihar Katsina ya amince da ci gaba da yi wa ma’aikatan jihar da na kananan hukumomi da malaman makarantun firamare da ya sanya a watannin baya sakamakon bullar cutar Korona da kuma karacin kudin shiga da jihar ta samu.

Bayanin hakan na kunshe a cikin wata takardar sanarwar da babban sakataren na ofishin shugaban ma’aikata na jihar Katsina, Usman Isiyaku ya sanyawa hannu.

Sanarwa ta kara da cewa a ranar 22/05/2020 da aka dakatar da duk wani karin girma ga ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi da malaman firamare. Gwamna Aminu Bello Masari ya amince a dage wannan dakatarwar a ci gaba da yiwa duk wani maaikacin da ya cancanci karin girma, domin kara masu kwarin gwiwa da bunkasa kwazon su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here