Masari Ya Biya Kudin Jarrabawar NECO Ta Daliban Sakandiren Jihar Katsina

Kwamishinan Ilimi na Jihar Katsina Professor Badamasi Lawal Charanchi

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari Ya Amince Da Biyan Naira Miliyan Dari Ukku Ga Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandire Ta NECO, Domin Ganin Sun Sako Sakamakon Daliban Da Hukumar Ta Rike, Saboda Rashin Biyan Kudin Ta Zangon Karatu Na Shekarar 2019 Zuwa 2020.

Kwamishinan Ilimi Na Jihar Katsina, Alhaji Badamasi Lawal Charanchi Ya Bayyana Haka A Yau Laraba.

Rashin Biyan Kudin Jarrabawar NECO Da Gwamnatin Jihar Katsina Ta Yi Ya Kawo Cece-kuce A Ciki Da Wajen Jihar Katsina. Inda Har Wasu Kungiyoyin Da Ba Na Gwamnati Ba Sun Fara Shirin Yin Wata Gidauniyar Kudi Domin Ganin Sun Biya Kudin Jarrabawar. Kashi Tamanin Cikin Dari Dai Iyayen Yara Suka Biya Wa Yaransu Kudin Jarrabawar.

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here