Advert
Home Sashen Hausa Masarautar Kano za ta naɗa Lamido Sunusi sarautar Wambai

Masarautar Kano za ta naɗa Lamido Sunusi sarautar Wambai

Masarautar Kano za ta naɗa Lamido Sunusi sarautar Wambai

Labarai24

Masarautar Kano ta sanya ranar 28 ga watan Mayun nan a matsayin ranar da za ta naɗa tsohon Chiroman Kano, Murabus wato Lamido Sunusi Ado Bayero a matsayin Wamban Kano.

Tun da farko shafin masarautar Kano na facebook ne ya wallafa sanarwar nadin na Lamido Sunusi Ado Bayero.

“Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zai nada dan uwansa kuma tsohon Chiroman kano murabus Alhaji Sunusi Ado Bayero, sarautar Wamban Kano, ranar juma’a 28/5/2021 da misalin karfe 10:00 na safe a fadar masarautar Kano. Allah ya sanya alkhairi Amin. Allah ya taimaki sarki ran sarki ya dade”

Lamido Sanusi Ado Bayero
Idan za a iya tunawa dai a cikin shekarar 2015 majalisar masarautar Kano ta sauke Alhaji Lamido Ado Bayero daga sarautar Ciroma, sakamakon rashin mubaya’a ga tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II.

Alhaji Lamido Ado Bayero, shi ne mutumin da ya yi takarar neman sarautar Kano da tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II, bayan mahaifinsa Alhaji Ado Bayero ya rasu.

Haka kuma tun da ya rasa kujerar Sarkin Kanon, majalisar masarautar ta ce bai yi mubaya’a ga sabon Sarkin ba.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

DRAFT APC CONVENTION TIMETABLE – Jan 16, 2022

1. January 17th - PMB Letter to CECPC on February National Convention and associated matters 2. January 18th -CECPC Meeting announcing National Convention date of...

Da ƊUMI-ƊUMI- Kotu ta umarci Rundunar Sojin Ƙasa da ta baiwa Nnamdi Kanu Naira biliyan 1

Wata Babbar Kotu da ke zaman ta a Umuahia ta baiwa Gwamnatin Taraiya da Rundunar Sojin Ƙasa da su baiwa Jagoran masu Rajin Samar...

THE RECONSTRUCTION OF THE APAPA – OWORONSHOKI – OJOTA EXPRESSWAY IS PROGRESSING EXPRESSLY!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/258361216380403/

Teenager kills man over football league supremacy

Teenager kills man over football league supremacy By Danjuma Michael, Katsina 19 January 2022   |   2:53 am A teenager, Idris Yusuf, 18, has allegedly killed a...