Manzanni sunzo daga Gwamnatin jihar Katsina, sun saukar maku da Wahayi akan Social Media- Dr Bashir Usman Ruwan Godiya

Sashin Ɗalibai da suka amfana da Horaswar ta wata uku

Zaharaddeen Mziag @Katsina City News

‘Yan jarida sune Dutsen murhu na huɗu ni a wajena, idan kace Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin jiha, Lokal Gwamment, to sai kace Press (amma fa a ra’ayina) Dakta Ruwan Godiya yayi wannan jawabin ne a wajen taron kammalawar Horo na watanni uku ga ma’abota kafar sada zumunta na Social Media suka samu a makarantar Hassan Usman Katsina Polytechnic (HUKPOLY) wanda Gwamnatin jihar Katsina ta dauki nauyi.

“Dan Adam duk inda yake yana buƙatar a saita shi, shi yasa ma da Allah ya halicci dan Adam be kyaleshi haka ba sai ya dunga aiko masa da Manzanni lokaci bayan lokaci domin su saita shi, zuwa ga daidai. Don haka ku ma ‘yan Social Media ga tawagar Manzanni daga Gwamnan Katsina Rt.Hon. Aminu Bello Masari sun zo maku da Wahayi akan Social Media, domin kusan Dai-dai a cikin sa kusan abinda ba dai-dai ba, saboda haka Manzanni sunzo sun isar da saƙo, idan a da’ baku balaga ba yanzu kun Balaga Al’ƙalami ya hau kanku” Dr Ruwan godiya, ya ƙara da cewa; “Kuma ku sani Social Media Takobi ce me kaifi biyu, ko ku yanka da Bisimilla kuci Halas! ko ku yanka ta ƙeya kuci mushe!

Taron wanda ya samu baƙunci Farfesa Mainasara Yakubu Kurfi (Shugaban Sashen koyar da aikin jarida na jami’ar Bayero dake Kano) da Dr. Mukhtar Alƙasim ABU Zaria, Dr Sama’ila Balarabe, sai Hon. Kabiru Sha’aibu (Me bawa Gwamnan Katsina shawara a kan sha’anin siyasa) da sauran manyan baƙi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here