Manyan Sojoji 45 sun mika takardun ajiye aiki saboda baiwa wanda ke kasansu shugabancin da Buhari yayi
Manyam sojoji 45 ne daga gidan sojin ruwa na sama dana kasa suka mika takardun ajiye aiki saboda baiwa sojojin dake kasa dasu a mukami shugaban cin da shugaba Buhari yayi.
Yawancin wamda suka mika takardun ajiye aikin suna da mukaman Birgediya janar da Majo janar ne daga rukunin sojoji na 33 da 35.
Sunnews ta gano cewa ajiye aikin bashi rasa nasaba da sabbin shuwagabannin tsaron da shugaba Buhari ya nada.
Wani tsohon soja ya bayyana cewa dama akan samu irin wannan lamari, kuma wanda ke sama da wanda aka baiwa mukamin shugabanci a baya yanzu shine zai rika girmama sabon shugaban.