Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Ƙasa, Abubakar Malami SAN, ya raba kyautar motocin zamani na-gani-na-faɗa ga masu yaɗa manufarsa a kafafen sadarwa, ƙungiyoyin yaƙin neman zaɓen sa da kuma abokan siyasar sa a Jihar Kebbi.

Ɗaya da ga cikin waɗanda su ka amfana da motocin ya shaida wa DAILY NIGERIAN cewa Malami ya taba motocin ne a wani ɓangare na shirye-shiryen baiyana takararsa ta gwamna a zaɓen 2023 a jihar.

DAILY NIGERIAN ta jiyo cewa Ministan ya raba motocin ƙirar Marcedes-Benz GLK guda 14 ga ƴan barandan sa da ke yaɗa manufofinsa a kafafen sadarwa su 14.

Hakazalika abokansa ma su 4 sun samu kyautar motoci ƙirar Lexus LX 570.

Sai kuma Shugabannin gidauniyoyi da kungiyoyin goyon bayan Malami da a ka raba wa Prado SUV da kuma Toyota Hilux, inda kowannen su ya samu guda ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here