Malamai kudaina hawa busa Mimbarin Addini kuna yaɗa jita-jita- Gwamnan katsina a wajen taron ƴan jaridu a jihar katsina.

Gwamnan katsina Rt. Hon. Aminu Bello masari yayi wan’nan kiran a wajen taron bita na ƴan jaridu da masu amfani da kafar sada zumunta ta zama (Social media) wanda Ofis ɗin mai bawa Gwamnan katsina shawara na musamman akan harkokin tsaro ya shirya.

Dayake gabatar da jawabi bayan tsokaci da yayi akan ƴan jaridar kansu da ‘yan (Social media) akan faɗar gaskiya, inda ya kawo mashahurin Hadisin Annabi (S) cewa (Ya ku waɗanda sukayi Imani kufaɗi Al’khairi ko kuyi shiru) yace indai har ba zaka taɓa faɗin Al’heri daga bakin ka ba to shuru yafi yimaka alheri. Yace “sai kuga mutum musulmi kuma da anyi kiran sallah shine gaba-gaba wajen sahun sallah amma dashi ake haɗa kai wajen kashe mutane da (da sace su)” yayi kira da jin tsoron Allah da aiki tsakani da Allah saboda adalci shine gaba ga komi.

Daya waiwayo akan malamai, Gwamna masari yace, Naso ace angayyaci malami a wan’nan taron duba da suma suna bada tasu gudumawar.

“Dayawa daga Malamai suna amfani da Mimbarin Firi huɗuba (Free khudba) suna yaɗa jita-jita ga Al’uma. Sai kaga malami Busa mimbari an faɗimasa Wai-wai! Kuma ya ɗauki wan’nan wai-wai ɗin a matsayin makamin yaƙar Gwamnati, basuyi mana uzuri ba, basu nememu sukaji ta bakin mu ba ta yiyu wanda yazo masu da labarin bashi da ko alaƙa da kansila ballantana wani jami’in Gwamnati.”

Taron da yasamu halartar manyan masana a harkar jarida Daktoci da ɓangaren ‘yan social media, ya gudana ne a babban ɗakin taro na ma’aikatar ƙananan hukumomi da ke daura da ginin majalisa a kan hanyar Kaita cikin garin katsina. Angudanar da taron bisa tsari da bin dokokin hukumar NCDC domin kaucewa yaɗuwar Covid-19.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here