Advert
Home Sashen Hausa MAKOFTAN MU: Ƴan Nijar Sun Koka Kan Bazuwar Ƴan Bindiga A Dazukan...

MAKOFTAN MU: Ƴan Nijar Sun Koka Kan Bazuwar Ƴan Bindiga A Dazukan Kasarsu

Mahukunta a Jamhuriyar Nijar sun koka a kan ƙara fantsama da ‘yan fashin daji suka yi, tun bayan ɗaukar matakan murƙushe su da wasu jihohin arewa maso yammacin Nijeriya mai maƙwabtaka da ita suka yi.

A baya-bayan nan hare-hare da satar mutane don neman fansa na ƙaruwa a yankin MadaRumfa na jihar Maradi.

Ko a ƙarshen mako, ‘yan fashin sun abka wani gari inda suka saci mutum biyar ciki har da mace huɗu bayan sun harbi mutane.

Sadissou Sani magajin garin Safo a cikin yankin na Maradi mai makwabtaka da jihar Zamfara ta Najeriya ya shaidawa wakiliyar BBC cewa ƴan bindigar sun daina satar dabbobi sun koma satar mutane a yankin.

Ya ce daga cikin mutane biyar da suka sace, hudu daga cikinsu mata ne.

Magajin garin na Safo ya yi kiran ƙara daukar matakai domin magance abin da ya kira babbar matsala.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...