DAGA: Cmrd Abubakar Ilya.

Da safiyar yau Lahadi, wanda yayi daidai da 01/05/2022. Jigon jam’iyyar PDP a jihar Katsina, wanda a kullum kare mutuncin jam’iyyar PDP da ‘ya’yanta ne aikin shi. Wato H.E Salisu Yusuf Majigiri (Garkuwan Gabas).

Majigiri, ya bayyana aniyar shi ta tsayawa takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin tutar jam’iyyar PDP mai alamar Lema. Inda taron ya gudana babban dakin taron sakatariyar PDP ta jiha dake cikin birnin Katsina.

Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP dake jihar Katsina, da kuma ‘yan takarkari na kujeru daban-daban dake fadin jihar ta Katsina. Haka zalika, taron ya hada da dukkan Shuwagabannin jam’iyyar PDP na kananan hukumomin jihar Katsina guda 34.

Tare da saurana masu jefa kuri’a na jam’iyyar PDP dake fadin jihar Katsina daga matakin karamar hukuma har zuwa Mazaba.

An gudanar da wannan taro cikin nasara domin kuwa anyi lafiya an gama lafiya.

Allah ya shige mana gaba, Ya bamu nasara a cikin wannan tafiya mai albarka. Allah ya tabbatar mana da Majigiri a matsayin sabon gwamnan jihar Katsina. Ameen👏

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here