Majalissar Dokokin Jihar Katsina Ta Amince Da Kirkiro Kwalejin Aikin Gona A Faskari.
A yau Talata kwamitin noma da albarkatun hadin guiwa da kwamitin Ilimi mai zurfi na majalissar dokokin jihar Katsina sun gabatar wa zauren majalissar dokokin jihar matsaya da gamsuwarsu a kan kirkiro Kwalejin aikin Gona da dan majalissa mai wakiltar mazabar karamar hukumar ta Faskari kuma Mataimakin Kakakin Majalissar Dokokin Jihar Hon Engr Shehu Dalhatu Tafoki ya gabatar har aka yi masa karatu na daya har zuwa na uku domin a kafa ta a garin Daudawa cikin karamar hukumar da yake wakilta ta Faskari.
A yau dai tuni majalissar ta aminta da kudurin kafa Kwalejin, za su mika shi zuwa majalissar zartarwa da gwamna ke jagoranta domin sa mata hannu a kama aikin bude makarantar gadan-gadan