Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da babban sakatare a ofishin shugaban ma’aikatan jihar Katsina Alhaji Usman Isyaku yasa ma hannu.

Sanarwar ta kuma umurci ma’aikatar lafiyar da ta fara aiwatar da gyaran da ya dace na dokokin gudanarwar Kwalejin Kimiyya da Fasaha da na Kwalejin Jiyya da Ungozoma na Katsina domin shigar da sabon tsarin.

Hakazalika, Majalisar zartaswar ta amince da daidaita tsarin gudanarwar manyan makaratun jihar da na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da Kwalejojin Ilimi na Gwamnatin Tarayya dangane da daukar aiki da kuma karin girma.

Majalisar ta kuma amince da kafa kwamitin rejista a karkashin ma’aikatar ilimi mai zurfi kan tsarin sauya sheka da jagorantar manyan makarantun biyu wajen bayar da shawara akan ma’aikatan da suka cancanci sauya sheka zuwa tsarin CONTEDISS 15 da karin girma bisa ka’idojin NBTE.

Don haka sanarwar ta bukaci dukkan wadanda za su ci gajiyar shirin da su kara kwazo wurin inganta ayyukan su don ganin an samu ci gaba a manyan makarantun kiwon lafiyar guda biyu dan amfanin al’ummar jihar Katsina.

Sanarwa daga Ofishin Shugaban ma’aikatan jihar katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here