Majalisar Zartaswar Jihar Katsina Ta Amince A Cire Wa Kowane Ma’aikaci Kudin Guddumuwar Tallafi Ga Yan Kasuwar Da Iftala’in Gobara Babbar Kasuwar Katsina

…jimlar guddumuwar da aka samu naira 152

Majalisar Zartaswar Jihar Katsina, karkashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari ta amince a cire wa kowane ma’aikacin gwamnatin jihar Katsina da na kananan hukumomin talatin da hudu da malaman makaranta wani kaso daga cikin albashinsu, domin baiwa yan kasuwar babbar kasuwar Katsina guddumuwa.

Kwamishinan Shari’a na jihar Katsina, kuma shugaban Kwamitin Aiwatar da aikin kwamitin da gwamnatin jIhar Katsina ta kafa, Barista Ahmad Usman El-marzuq ya bayyana wa manema labarai hakan, bayan kammala zaman majalisar zartaswa da gwamna Aminu Bello Masari ya shugabanta a yau Laraba a gidan gwamnatin jihar Katsina.

Barista Ahmad Usman El-marzuq ya kara da cewa za’a cire kaso ukku cikin dari daga Ma’aikaci dake mataki na daya zuwa mataki na goma sha hudu. Haka zalika, za’a cire wa gwamna da Kwamishinoni da masu baiwa gwamna shawara da masu taimaka masa na musamman da kuma sauran masu rike da mukaman Siyasa, za’a cire masu kaso ashirin na albashinsu cikin dari.

Da ya juya kan tallafin da guddumuwar da yan kasuwar babbar kasuwar Katsina suka samu, an samu naira Miliyan 152, wasu sun shigo hannu, Wasu kuma ba su kai ga zuwa hannu ba. Kwamitin ya gano yan babbar kasuwar Katsina sun yi asarar naira Miliyan dari tara da biyu, jimlar asarar da gobarar ta haifar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here