Majalisar Wakilan Najeriya ta yi watsi da neman a tsige Buhari

Majalisar Wakilan Najeriya ta yi watsi da kiran da wani ɗan majalisar ya yi na a tsige Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari daga mulki.
Honorabul Kingsley Chinda mai wakiltar mazaɓar Obio/Akpor ta Jihar Rivers da ke kudancin Najeriya ya nemi ‘yan Najeriya da su matsa wa wakilansu a majalisa da su fara shirin tsige Buhari daga mulki ranar Lahadi.
Sai dai mai magana da yawun Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, ya bayyana kiran ɗan majalisar da cewa “ra’ayin mutum ɗaya ne kawai daga cikin jam’iyyar adawa”.
“Da a ce wannan kiran bayan zuwan Buhari majalisa ne kuma ya gaza yin cikakken bayani ko kuma ya ƙi ɗaukar shawararmu, sai a ce kiran ya yi ma’ana,” in ji Benjamin Kalu cikin wata sanarwa.
A makon da ya gabata ne majalisar ta daddale sannan ta yi kira ga Shugaba Buhari da ya bayyana a gabanta domin yin bayani kan halin rashin tsaro da ƙasar ke ciki.
Matsalar tsaron da ake ciki ta ƙara ta’azzara a kwana nan sakamakon hare-haren ‘yan fashin daji a arewacin ƙasar da kuma yankan rago da Boko Haram ta yi wa manoma 43 a Zabarmari ta Jihar Borno, abin da ya sa majalisar ta gayyace shi.
Duk da cewa majalisar ba ta faɗi sanda take so shugaban ya je ba, ana sa ran ya bayyana a wannan makon bayan Kakakin Majalisa Femi Gbajabeamila ya ce Buharin ya yarda zai amsa gayyatar – kodayake shi ma bai faɗi rana ba.