Majalisar Tarayyar Amurka ta amince da nasarar Joe Biden

Majalisar Tarayyar Amurka ta amince da nasarar Joe Biden a zaɓen Amurka da aka gudanar a Nuwambar bara.
Kafin amincewar, majalisar wakilan ƙasar ta yi ƙuri’a domin yin watsi da koken da aka gabatar kan zaɓen jihar Pennsylvania inda aka samu ƙuri’a 282-138.
Tuni dama majalisar dattijan ta yi watsi da wannan koken.