Majilisar Dokoki ta Jihar Zamfara ta amince da samar da ƙarin madauri biyu a jihar.

Hakan yazo ne bayan kwaskwarima da a ka yi wa dokar kafa masarautu ta 15 ta 2000, wacce ta bada damar kafa masarautu a jihar.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran Majalisar, Nasiru Biyabiki ya fitar a jiya Juma’a a Gusau.

Biyabiki ya ce majalisar ta amince da kafa sabbin masarautun ne a zaman ta da ta yi.

Ya ce masarautun biyu da za a samar su ne Yandoton Daji da Bazai.

A cewar sa, masarautar Yandoton Daji, mai Sarki mai daraja ta biyu, ta haɗa da gundumomin Yandoton Daji, Keta, Kizara, Bawa-Ganga, Kwaren-Ganuwa, Danjibga da Kunchin-Kalgo, inda ya ƙara da cewa garin Birnin ‘Yandoto shine zai zama shelkwatar ta.

Yayin da masarautar Bazai, ita ma mai Sarki mai daraja ta biyu kuma shelkwatar ta a garin Jangeru, za ta haɗa da gundumomin Bazai, Jangeru, Galadi, Katuru, Birnin Yaro Tungar Kaho da kuma Tubali.

“Da ya ke gabatar da kudirin a zaman majalisar, Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye, Nasiru Bello Lawan (APC, mazaɓar Bagudu ta yamma) yayi kira ga ƴan Majalisar da su bada goyon baya a samar da masarautun.

“Lawan ya yi kira kan buƙatar gyaran dokar da ya ce an samar da ita shekaru 22 da su ka gabata.

“Dukkan ƴan Majalisar sun goyi bayan gyaran dokar domin samar da masarautun, inda su ka ce hakan zai bunƙasa rayuwa da tattalin arzikin al’ummar yankunan,”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here