Majalisar Dokokin Najeriya ta ɗaga ranar komawa bakin aiki

Hukumar gudanarwar Majalisar Dokokin Tarayyar Najeriya ta ɗaga ranar komawar ‘yan majalisar bakin aiki daga ranar 26 ga watan Janairu 26 zuwa 9 ga watan Fabrairu, 2021.

Hukumar ta bayyana haka ne a sanarwar da Akawun Majalisar Dokokin, Ojo Amos, ya fitar ranar Asabar.

Ya ce an ɗaga ranar komawar ‘yan majalisar bakin aiki ne domin bai wa ‘yan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) damar sake yin rijistar kasancewa mambobin jam’iyyar.

Hukumar gudanarwar Majalisar Dokokin Tarayyar ta nemi afuwar sauran ‘yan jamai’ar bisa wannan jinkiri na komawa bakin aiki.

A watan Disamba ne ‘yan majalisar dokokin suka tafi hutun Kirsimeti da sabuwar shekara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here