Majalisar Dokokin jihar katsina ta zartar da wa’adin shekara biyar ga wasu jami’an gudanarwa na jami’ar Umaru musa

MAJALISAR DOKOKI TA JIHAR KATSINA TA ZARTAR DA DOKAR WA’ADIN SHEKARA BIYAR TARE DA KARIN SHEKARA DAYA GA WASU MANYAN JAMI’AN GUDANARWAR JAMI’AR UMARU MUSA YAR’ADUA DAKE NAN KATSINA.

A zaman majalisar Dokoki ta Jihar Katsina na ranar Laraba 24/02/2021 kalkashin jagorancin kakakin Majalisar Rt. Hon. Tasi’u Musa Maigari Zango, majalisar Dokokin ta zartar da Dokar wa’adin shekara biyar kadai da kuma karin shekara guda ga wasu daga cikin Jami’an gudanarwar Jami’ar Umaru Musa Yar’adua dake nan Katsina.

Zartar da Dokar da majalisar tayi ya biyo bayan karanta dokar karatu na uku tare da gabatar da Rahoto kan Dokar da shugaban Kwamitin kula da Ilmi Mai Zurfi na Majalisar Hon. Shamsuddeen Abubakar Dabai ya gabatar a gaban zauren majalisar yau Laraba. Kudirin dokar na shekara ta 2020 zuwa 2021, majalisar ta tabbatar da ita, abinda ya rage a turama Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt in. Hon. Aminu Bello Masari ya sanya mata hannu ta cigaba da aiki.

Da yake ma manema labarai karin bayani bayan zaman majalisar shugaban Kwamitin kula da ilmi Mai Zurfin na Majalisar Hon. Shamsuddeen Dabai ya bayyana cewa” gyaran Dokar Jam’iar Umaru Musa Yar’adua mallakin Gwamnatin Jihar Katsina, ya biyo bayan gyaran Dokar jami’o’in kasar nan dake kalkashin Gwamnatin Tarayya da majalisar Dokoki ta Tarayya tayi, na wa’adin shekara biyar kadai tare kuma da karin shekara daya ga wasu Manyan Jami’an gudanarwar Jami’o’in kasar nan. Wadanda Dokar ta shafa sun hada da, Rajistara, Laberiyan, da Basa.

Duk a zaman majalisar Dokokin na yau Laraba, majalisar ta tantance Kwamishina na dindin na Hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Katsina, Alh. Amadu Ibrahim Kaita shine sabon Kwamishinan na dindin na Hukumar zaben da majalisar ta tantance. Alh. Amadu Ibrahim Kaita ya fito ne daga karamar hukumar Kaita, ita dama kujerar Dan karamar hukumar Kaita ne yake rike da ita kafin sabunta ta ga Alh. Amadu Ibrahim Kaita, Marigayi Hon. Aliyu Ibrahim Kaita shine yake rike da kujerar kafin Rasuwar shi ranar 7/12/2020.

Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Kaita Hon. Musa Nuhu Abdullahi Gafia shine ya bayyana halaye masu kyau ga wanda aka tantancen, kuma ya nemi alfarmar abokan aikinshi ‘yan majalisar dasu amince da wanda aka tantancen, kasancewar shi wanda yake da kwarewa a wannan bangare, kuma mutum ne mai gaskiya da rikon amana. Bayan ‘yar gajeruwar muhawara da ‘yan majalisar sukayi kan wanda aka tantancen, daga karshe sun amince da bukatar Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Kaita da wanda aka tantancen ya fito…. An wanke Alh. Amadu Ibrahim Kaita a matsayin mukamin Kwamishina na dindin na Hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Katsina ba tare da wata doguwar muhawara da tambayoyi ba.

Rahoto
Surajo Yandaki
Edita, Mobile Media Crew
24, February 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here