Advert
Home Sashen Hausa Majalisar dokokin jihar katsina ta gabatar da wani ƙuduri na musamman don...

Majalisar dokokin jihar katsina ta gabatar da wani ƙuduri na musamman don yabama mai girma Gwamna Aminu Bello masari.

MAJALISAR DOKOKI TA JIHAR KATSINA TA GABATAR DA KUDIRI NA MUSAMMAN DON YABAMA MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR KATSINA KAN RABA KAYAN TALLAFIN CORONA VIRUS GA AL’UMMAR JIHAR KATSINA CIKIN LOKACIN DA YAKAMATA.

A zaman majalisar Dokoki ta Jihar Katsina na yau Talata 10/11/2020 wanda Mataimakin kakakin majalisar Rt. Hon. Shehu Dalhatu Tafoki ya jagoranta, an gabatar da wasu kudirori guda bakwai (7). Kudirorin da aka gabatar sun hada da!

(1) KUDIRI NA FARKO = Kudirin doka ne na gyaran dokar ma’aikatan Gwamnatin Jihar Katsina ta 2020 a karatu na biyu (Second Reading) a turance, wanda yan majalisa guda takwas (8) suka dauki nauyi, wanda suka hada da.

Hon. Engr. Shehu Dalhatu Tafoki, Dan majalisa Mai Wakiltar Karamar Hukumar Faskari
Hon. Abubakar Suleiman Abukur, Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Rimi
Hon. Musa Nuhu Gafia, Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Kaita
Hon. Nasir Yahaya Daura, Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Daura
Hon. Shamsuddeen A. Dabai, Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Danja
Hon. Ibrahim Umar Dikko, Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Matazu
Hon. Sani Lawal Baure, Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Baure
Hon. Lawal H. Yaro, Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Musawa.

(2) KUDIRI NA BIYU = Kudirin doka ne na dokar tara kudaden shiga na Jihar Katsina wuri daya, dokar shekara ta 2020, itama anyi mata karatu na biyu (Second Reading) a turance. Shugaban masu Rinjaye na Majalisar kuma Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Rimi Hon. Abubakar Suleiman Abukur Korau ya karanta.

(3) KUDIRI NA UKU = Kudiri ne na gabatar da wani Rahoto na Komiti na musamman da majalisar ta kafa don binciken kudaden Albashin ma’aikatan Shara’a na Jihar Katsina wanda ofishin Babban akawunta na Jihar Katsina yayi, wanda shugaban komitin na musamman Hon. Lawal H. Yaro Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Musawa ya gabatar.

(4) KUDIRI NA HUDU = Kudiri ne na gabatar da Rahoton kokarin Komitin kulada harkokin Addini na Majalisar Dokokin Jihar Katsina daga 01/July/2020 zuwa 30/September/2020. Wanda shugaban komitin Hon. Mustapha Yusuf Jibia Dan Majalisa Mai Wakiltar Karamar Hukumar Jibia ya gabatar.

(5) KUDIRI NA BIYAR = Kudiri ne na Yabama Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari da majalisar tayi. Yabon Gwamnan ya biyo bayan wasu al’amurra da suka faru baya, bayan nan na zanga, zangar End Sars, da matasan kasar musamman na kudancin kasar nan sukayi, inda suka rika bude rumbunan ajiyar kayan abinci na Gwamnati a wasu jihohin kasar nan, suna dibar kayan abinci na tallafin Coronavirus da Gwamnatin Tarayya ta kawo, a raba ma Al’umma don rage masu radadi na zaman gida na lokacin Coronavirus.

Kusan wata biyu da suka gabata, Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya bada umurnin raba kayan tallafin Coronavirus ga Al’ummar Jihar Katsina da Gwamnatin Tarayya ta aiko, Wanda cikin yabon Gwamnan da majalisar tayi, sun kira Gwamnan da Dattijo mutunen kirki wanda ya fidda Al’ummar Jihar Katsina kunya kan abubuwan da suka faru lokacin zanga, zangar, End Sars, na bude rumbunan ajiyar kayan abinci na tallafin Coronavirus a wasu jihohin kasar nan.

(6) KUDIRI NA SHIDDA = Kudiri ne da Dan Majalisa mai wakiltar karamar hukumar Mani Hon. Aliyu Sabiu Muduru ya gabatar kan yana kira ga majalisar zartarwa ta Jihar Katsina data gaggauta daukar Malaman koyar da harshen Larabci da ilmin Addinin musulunci a Makarantun firamare da sakandire na Jihar Katsina saboda karanci da sukayi a Makarantun mu.

Da yake gabatar da jawabin shi wajen gabatar da kudirin Hon. Aliyu Sabiu Muduru ya bayyana “cewa mafi yawancin Makarantun Gwamnati tun daga firamare da sakandire, zakaga makaranta mai dabili dubu uku, amma bai wuce ka samu malami mai koyar da harshen Larabci da ilmin Addinin musulunci guda biyu ba. Wanda wannan barazana ne ga tarbiyar yayanmu a Addinance. Dukkan yan majalisar da suka tofa albarkacin bakinsu kan kudirin sun yaba ma Hon. Aliyu Sabiu Muduru kan nazari mai Zurfi da yayi ya gabatar da wannan kudiri mai matukar fahimci, wanda ya shafe kowa da kowa. Daga karshe Kakakin majalisar yaba Komitin harkokin Ilmi da Komitin harkokin Addini na Majalisar alhakin duba matsalar tareda gabatar ma da majalisar Rahoto.

(7) KUDIRI NA BAKWAI = Kudiri ne da Dan Majalisa Mai Wakiltar Karamar Hukumar Daura Hon. Nasir Yahaya Daura ya gabatar yana kira ga majalisar zartarwa ta Jihar Katsina data samar da Makarantar koyon aikin kiwon lafiya (SCHOOL OF NURSING) a turance, a garin Daura da Garin Funtua. Dan majalisar na Daura Ya gabatar da wannan kudiri na neman wannan makaranta don fadada Makarantun koyon aikin kiwon lafiya a Jihar Katsina, don bada dama ga yan Jihar Katsina dayawa masu sha’awar shiga Makarantun koyon aikin kiwon lafiya. Bayan tattauna kudirin, daga Karshe kakakin majalisar ya bada umurni ga komitin kulada harkokin kiwon lafiya na Majalisar ya duba kudirin tareda gabatar ma da majalisar Rahoto.

Rahoto.
Surajo Yandaki
Edita, Mobile Media Crew
10, November 2020.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Har yanzu: Gwamna Masari na Alhinin Rasuwars Kwamishinan Kimiyya Rabe Nasir

Gwamna Aminu Bello Masari ya kara bayyana rasuwar Dokta Rabe Nasir a matsayin babban rashi duba da yadda yake da jajircewa tare da sadaukarwa...

Katsina lawyer in court over alleged cheating,forgery, impersonation

A Funtua based Company in Katsina state, NAK International Merchant has dragged a Lawyer, Barrister Mahdi Sa'idu to court over alleged cheating, forgery and...

The YOUTHS ASK YAHAYA BELLO FOR PRESIDENT MOVEMENT (YAYBP) under the Leadership of their Founder/National Coordinator Alhaji Ibrahim Muhammad on Saturday 15th January, 2022...

The movement, which said the gesture is part of its efforts to alleviate the sufferings of the less privileged in the society through its...

Bin Sa’id Tsangaya Model School Ta Yi Bikin Saukar Dalibai.

Daga Auwal Isah. A karon farko, Makarantar hardar Alkur'ani mai tsarki ta " Bin sa'id Tsangaya Model School " da ke a unguwar Tudun 'yan...

Sanata Bola Ahmed Tinubu Ya Kawo Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Kwamishina Rabe Nasir A Jihar Katsina

Ziyarar Da Jigon Jam'iyyar APC Na Kasa, Tsohan Gwamnan Jihar Legas, Sanata Bola Ahmed Tinubu Ya Kawo A Jihar Katsina, Domin Yin Ta'aziyyar Rasuwar...