Daga Usman Salisu Gurbin Mikiya

Majalisar Dokokin Jahar Lagos a ranar Litinin tayi gyaran Dokar Masu Manyan Laifi akan a daina holen su a Kafafen Yada Labaru.

Mataimakin Shugaban Majalisar Wasiu Eshilokun-Sanni ya gabatar da kudirin a lokacin zaman Majalisar a ranar Litinin.

Eshilokun-Sanni yace sashi na 9 (A) na sabuwar dokar da aka gabatar, Yansanda zasu daina holen masu laifi a Kafafen Yada Labaru.

“Kudirin ya Kuma bayar da matakan da Yansanda zasu kama mutum, ba tare da bayar da dama ba, daya daga cikinsu shine Sayar da Makamai ko kuma wasu abubuwa masu hadari.

Mataimakin Shugaban Majalisar ya Kuma yi nuni dacewa, Mai laifi na bukatar a rika bashi kulawa irin ta mutane ba tare da wulakantawa ba.

Bayan kuri’ar goyon baya da aka kada a zauren Majalisar, Mataimakin Shugaban Majalisar ya umarci Akawun Majalisar Mr. Olalekan Onafeko, daya gabatar da Dokar ga Gwamna Babajide Sanwa-Olu domin sanya mata hannu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here