Majalisar Dinkin Duniya, karkashin shugabancin Antonio Gutterres ta amince da sake nada Amina Muhammad, mataimakiyar sakatare janar na wasu shekaru biyar masu zuwa.

An sake zaɓen tsohuwar ministar muhalli ta Najeriya Amina Mohammed a matsayin mataimakiyar sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya.

A ranar Juma’a ne babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya sake zaɓen Antonio Guterres a matsayin Sakatare Janar a wa’adi na biyu na shekara biyar.

Kuma zai ci gaba da aiki tare da Amina Mohammed ƴar Najeriya daga jihar Gombe, a matsayin mataimakiyarsa, kamar yadda ta sanar a shafinta na Twitter.

Guterres da Amina za su fara sabon wa’adi a farkon watan Janairun 2022.

Antonio Guterres ya gaji Ban Ki-moon ne a watan Janairun 2017 kafin Donald Trump ya zama shugaban Amurka wanda ya sha caccakar Majalisar Dinkin Duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here