Majalisar dattijan Najeriya ta amince da nadin sabbin hafsoshin tsaron kasar

Majalisar Dattijan Najeriya ta amince da nadin sabbin hafsoshin tsaron kasar da shugaba Muhammadu Buhari ya mika mata.

A wani zama da ta yi a ranar Talata Majalisar ta tattabar da nadin, kamar yadda mai taimakawa shugaba Buhari kan kafafen sada zumunta Bashir Ahmed ya wallahafa a shafinsa na Twitter.

A watan Janairu ne ne Shugaba Buhari nada sabbin manyan hafsoshin sojin kamar haka: Janar Leo Irabor, babban hafsan tsaro; Janar I. Attahiru – babban hafsan sojan ƙasa; Rear Admiral A.Z Gambo – babban hafsan sojan ruwa; da kuma Air-Vice Marshal I.O Amao – babban hafsan sojan sama.

Sun maye gurbin Janar Abayomi Olonisakin, Tukur Buratai, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas; Air Marshal Sadique Abubakar wadanda ya nada a 2015 bayan ya lashe zabe a karon farko.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here