Majalisar Ƙoli ta Musulmin Najeriya ta hana yin I’tikaf

Majalisar Ƙoli ta Musulmi a Najeriya, NSCIA ƙarƙashin jagorancin Mai alfarma Sarkin Musulmi ta bukaci a dakatar yin I’tikaf lokacin azumi saboda annobar korona.

Sanarwar da Majalisar ƙolin ta wallafa a Twitter ta yi kuma yi kira ga al’ummar musulmi su kiyaye matakan rage yaɗuwar korona musamman bayar da tazara tsakani a lokacin azumin Ramadan.

Tuni kwamitin ganin wata a Najeriya ya fitar da sanarwar cewa a ranar Litinin ne za a fara duban watan azumi a ƙasar.

A ranar Talata kuma Al’ummar Musulmi ke fatan soma Azumin watan Ramadan.

Social embed from twitter

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here