Mai yiyuwa Gwamnatin Najeriya ta bude kan Iyakokinta da kasashen ketare…

Ministan kudin Najeriya Hajiya Zainab Shamsuna Ahamad

Ministan kudi da tsare tsare itace ta bayyana haka ga mamema labarai a fadar Gwamnatin Nijeriya bayan taron sati sati da ake gudanarwa a fadar Shugaban Kasar.

Shamsuna ta ce kwamitin da Gwamnatin ta kafa domin yayi duba akan lamarin kan Iyakokin kasar ya kammala aikin sa kuma yana gab da mika Rahoton shi, sai dai Ministan bata Ambaci lokacin da kwamitin zai gabatar da Rahoton nashi ba.

Najeriya dai ta ayyana kulle kan Iyakokin ta ne a cikin watan Agustan Shekarar Dubu Biyu da Sha Tara, Inda akayi zargin cewa ana safarar makamai da miyagun kwayoyi ta kan Iyakokin na Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here