Advert
Home Sashen Hausa Mai Turaka Ya Gwangwanje Al'ummar Unguwar Daki-Tara Da Wani Muhimmin Aiki.

Mai Turaka Ya Gwangwanje Al’ummar Unguwar Daki-Tara Da Wani Muhimmin Aiki.

Mai Turaka Ya Gwangwanje Al’ummar Unguwar Daki-Tara Da Wani Muhimmin Aiki.

@Katsina City News

Mai bawa Gwamnan Katsina shawara kan wayar da kan Al’umma Alhaji Abdul-aziz mai turaka, ya gwangwaje al’ummar Unguwar Daki-tara da wata hanyar ruwa.

Hanyar ruwan wadda ta haura tsawon mita 300 a cikin wani lungu da ke cikin unguwar, ya faranta wa al’ummar yankin ba kadan ba.

Da muke zantawa da mazauna Unguwar, sun bayyana mana jin dadinsu matuka, sun kuma yi masa fatan alkhairi da fatan ci gaba da gudanar da irin wadannan ayyuka na alkhairi, sun kuma sha alwashin kiyayewa tare da tsare aikin yadda ya kamata don dorewar amfanuwar jama’ar yankin bakiɗaya

A ta bakin al’ummar unguwar, sun ce, sun sha mika ƙoƙon barararsu ga masu hannu-da-shuni domin yi masu magudanar ruwan wadda a lokacin damina ruwa na yi masu illa a gidajensu, amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba sai yanzu da S.A mai turaka ya gwangwaje su da yi masu hanyar ruwan ba tare da sun kai masa ƙoƙon bararsu ba kamar yadda suka sha yi ga wasu mutane a baya.

Unguwar daki tara dai na cikin unguwannin da ke fama da karancin magudanan ruwa da kwatoci a birnin Katsina, lamarin da ke ci wa jama’a tuwo a kwarya, duk da kokarin da gwamnati ke yi wajen giggina wasu sabbin magudanan ruwan a wasu yankuna a dan tsakanin nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

BALA ABU MUSAWA NE ZABINMU ~~~Gamayyar Kungiyoyin Goyon Bayan APC na Shiyyar Daura

Daga Bishir Mamman @ katsina city news Kungiyar wadanda suke da wakilci a kananan hukumomin yankin sanatan Daura, karkashin shugabancin Sani Abdurrahman da mataimakiyarsa Hadiza Mamman. Suna...

POLICE ARREST SEVEN FOR KIDNAP, INFORMANTS.AND SUPPLY OF FUEL

Hassan Male @ Katsina city news The Katsina State Police Command had on the 18/9/2021 succeeded in arresting one Lawal Shu’aibu ‘m’ aged 32 years of...

ARREST OF SUPPLIERS OF FUEL TO BANDITS

On the 18/9/2021 based on credibleintelligence, the command succeeded in arresting (1) Lawal Shu'aibu 'm' aged 32 years of Maradi, Niger Republic. Conveying fuel...

SHARHIN: Katsina City News ZABEN SHUGABANNIN APC A KATSINA

SHARHIN: Katsina City News ZABEN SHUGABANNIN APC A KATSINA ...A tabbatar Da An Yi Adalci *Jinjina Ga Gwamnan Katsina Da Alhaji Muntari Lawal @Katsina City News Ranar Asabar 2...
%d bloggers like this: