Mai Shafin twitter yagoyi bayan #EndSars

Mai kamfanin twitter shima ya goyi bayan kawo ƙarshe Rundunar Sars ta Nigeriya

Mai shafin Twitter ya goyi-bayan zanga-zangar #EndSars

Jack

Mutumin da ya samar da shafin Twitter, Jack Dorsey ya nuna goyon-bayansa ga zanga-zangar #EndSARS da ke ci gaba da jan hankali a Najeriya

Dorsey ya sake wallafa bayanan asusun tara kuɗin tallafawa zanga-zangar a shafinsa @jack dauke da alamar tutar Najeriya.

Sannan ya sake wallafa wasu maƙaloli da ke nuna goyon-bayan zanga-zangar.

Sai dai wannan alamari ya janyo yabo da suka a shafin na sadarwa abin da ya kai ga wani mamba a Jam’iyyar APC, wanda kuma ya taɓa neman takara shugaban ƙasa Adamu Garba barazanar kalubalantarsa a kotu inda zanga-zangar ta kazance.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here