Matata Ta Tsufa Kuma Bata Biya Min Buƙatata Shi Yasa Na Koma Kwanciya Da Ɗiyata A Madadinta, Inji Mahaifin Da Aka Cafke Yana Lalata Da Ƴarsa Mai Shekaru 12

…mahaifina ya fara lalata da ni tun ina ƴar shekara 7, Inji yarinyar

Ƴan sanda sun kama wani mutum mai shekaru 49 a jihar Ogun bayan da ƴarsa ta kai rahoton cewa yana yin lalata da ita tsawon shekaru biyar.

Yarinyar mai shekaru 12 ta faɗawa ƴan sandan cewa mahaifinta ya fara kwana da ita tun tana ƴar shekara bakwai.

Ƴan sanda sun ce Ubong Williams Akpan ya yi ikirarin cewa matar sa ta tsufa kuma ba ta iya biya masa buƙatar sa, saboda haka ya koma kwanciya tare da ƴarsa a madadinta.

Jami’an tsaro sun cafke shi a ranar 2 ga Maris lokacin da yarinyar ta kai rahoton lamarin ga babban jami’in ƴan sanda na shiyyar a hedkwatar reshen Itele Ota, Monday Unoegbe, wani babban Sufeton ƴan sanda (CSP).

Ta faɗawa ƴan sanda cewa mahaifinta ya ci gaba da amfani da ita har tsawon shekaru biyar har sai da ta kasa jurewa kuma dole ne ta kai ƙara ga ƴan sanda.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Edward Ajogun ya ba da umarnin a tura ƙarar zuwa sashen tallafa wa iyali na rundunar Ota don cigaba da bincike da kuma gurfanar da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here