Magidanci ya sari matarsa mai ciki da ƴaƴanta a Kano

Rundunar ƴan sanda jahar Kano ta tabbatar da kama wani magidanci da zargin saran matarsa mai ciki wata goma da ƴaƴanta bayan da wata kotu ta raba aurensu.

Yan sanda sun ce sun kama shi ne bayan da suka jiyo kururuwar tsohuwar matar tasa da aka raba auren nasu a ranar Litinin din makon da muke ciki, bayan ta nemi dauki.

Abin ya faru ne a karamar hukumar Rano lokacin da matar ta kai karar mijin da ke cin zarafinta, dalilan da suka sanya alkali raba auren.

Matar mai suna Shafa’atu Sale ta ce an kammala shari’ar ba jimawa mijinata ya bi ta da wuƙa ya ɗaɗɗaɓa mata.

Yanzu haka dai Shafa’atu na kwance a asibitin Rano tana karban kulawa, yayinda su kuma jami’an tsaro ke zurfafa bincike.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun irin wannan korafi ko zargin cin zarafi da magidanta ke aikatawa a kan matarsu ba a Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here