Advert
Home Sashen Hausa Maganar Gwaggo ba wacce za'a yiwa biyayya bace a yanzu ~ Muaz...

Maganar Gwaggo ba wacce za’a yiwa biyayya bace a yanzu ~ Muaz Magaji

Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Muaz Magaji Dan Sarauniya, wanda yake neman jam’iyyar APC ta bashi tikitin takarar gwamnan jihar Kano a zaben shekarar 2023 mai zuwa, yace baza su yadda a kakaba musu gwamna a Kano ba, musamman wanda Gwaggo take magana akansa, domin korarsa akayi daga makaranta a lokacin da yake karatu.

Idan baku manta ba, a jiya jaridar Kano Online News ta rawaito cewa, mai dakin gwamnan Kano, Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje, tace su kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sule Garo, ne zasu gaje su a mulkin Kano, lamarin da ya janyo cece-kuce tsakanin magoya bayan gwamnati, kasancewar akwai masu zawarcin kujerar da dama cikin jam’iyyar APC.

Dan Sarauniya yana cikin mutanen da suka soki lamirin maganganun Gwaggo, yace a wannan karon dai suna da jaa, kuma ai dama akwai derby tsakanin Kano da Hadejia.

Daga: Kano Online News

15/8/2021

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Alleged Defamation: Gov. Masari demands N10bn, apology from journalists

Gov. Aminu Masari of Katsina State has demanded the payment of N10 billion as damages from Mr. Emmanuel Ogbeche and Mr. Ochaika Ugwu, Chairman...

Biliyan Ɗari shida da Miliyan ɗari biyu da Hamsin, Tallafi daga Gwamnatin Tarayya domin ɓunƙasa Karkara da gandun Daji a jihar Katsina…..

Biliyan Ɗari shida da Miliyan ɗari biyu da Hamsin, Tallafi daga Gwamnatin Tarayya domin ɓunƙasa Karkara da gandun Daji a jihar Katsina..... A ranar Alhamis...

DIRECTOR-GENERAL INAUGURATES NYSC MEGA PRINTING PRESS

NYSC Director-General, Major General Shuaibu lbrahim today inaugurated the NYSC Mega Printing Press in Kaduna. He said the project, which was conceived almost a decade...

Shugaba Buhari Ya Miƙa Ta’aziyyarsa Ga Iyayen Hanifa, Yarinyar Da Aka Kashe A Kano.

Daga Zaharaddeen Gandu Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina wa 'yan sandan Jihar Kano game da gano wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar mai...