A yau Litinin ne Ma’aikatar Kasafin Kuɗi Da Tsare-tsaren Tattalin Arzikin Jihar Katsina, karkashin Kwamishinanta Alhaji Faruq Lawal Jobe, inda shugabanni da daraktocin Hukumomin da ma’aikatun Gwamnati ke bayyana gabansu domin kare kasafin Kuɗin da su ka sa ran kashewa a shekarar mai kamawa ta 2022 idan Allah ya kaimu.

Kare kasafin na gudana ne a wurin Safkar Shugaban Kasa na tsohan Gidan Gwamnatin Jihar Katsina, karkashin jagorancin kwamishinan Faruq Lawal Jobe.

Da yake jawabin a wajen fara aikin, kwamishinan Faruq Lawal Jobe ya ce duk shekara ma’aikatu da sassan Gwamnatin domin su kare ayyukan da suke shirin yi a shekarar 2022.

Alhaji Faruq Lawal Jobe ya kara da cewa tana duba wasu hanyoyin karin kuɗin domin ganin ai aiwatar da ayyukan da aka kudiri niyyar yi a jihar Katsina.

Shugaban Kwamitin Kare kasafin Kuɗin kuma kwamishinan Kasafin Kuɗi Da Tsare-tsaren Tattalin Arzikin Jihar Katsina ya ce Ma’aikatar ta karade kananan hukumomin talatin da hudu na jihar Katsina, inda aka kara ilmantar da al’umma da kuma gabatar da ayyukan da suke bukata daga gwamnati kai tsaye da jami’an Ma’aikatar.

An fara kare kasafin kudin da Ofishin mataimakin gwamna, karkashin jagorancin babban sakataren, Aminu Abu Bazariye. Tuni dai ma’aikatu da sassan Gwamnatin jihar Katsina sun hallara domin ganin sun kare kasafin kuɗinsu na shekarar 2022.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here