Ma’aikatan tarayya za su ci gaba da aiki daga gida a Najeriya

Buhari da Folashade
Copyright:NG

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta umarci ma’aikata a mataki na 12 zuwa ƙasa da su ci gaba da aiki daga gida har zuwa ƙarshen watan Maris.

Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Dr. Folashade Yemi-Esan, ita ce ta bayar da umarnin cikin wani jadawali da ta fitar ranar 3 ga watan Maris mai taken “An Tsawaita Umarnin Aiki daga Gida”.

A cewarta, duk da cewa an samu raguwar masu kamuwa da cutar korona, abu ne mai muhimmanci a ci gaba da aiki daga gidan.

Mutum 18 ne suka mutu a jiya Laraba a Najeriya sakamakon cutar ta korona sannan wasu 464 suka kamu.

Jumillar mutum 156,963 ne suka kamu da cutar tun bayan ɓullarta Najeriya a watan Fabarairun 2020.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here