Sanata Ali Ndume ya mayarwa da shugaban sojojin Nigeria Tukur Yusuf brutai martani.
Daga Kabiru Ado Muhd
Dayake bayani yau a Abuja, sanata Ali Ndume yace Sam Sam shugaban sojojin Nigeria Tukur Yusuf brutai baiyiwa yan uwansa sojoji adalci ba bisa zargin su da hada baki da wasu manyan yan siyasar kasar nan wajen shirya juyin mulki a karkashin kasa.
Sanata Ali Ndume yace Tukur Yusuf brutai yayi amfani da wannan furucin da yayi ne kawai don ya wanke kansa da gazawar da suka nuna wajen rashin iya tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al ummar Nigeria musamman arewa maso gabashin kasar.
Ali Ndume yace halin da ake ciki yau a Nigeria duk duniya ta tabbatar da irin gazawar da shugabannin tsaron kasar nan sukayi Na rashin iya kawo karshen ta addaci kamar yadda jam iyarsu ta APC tayi alkawari.
A wasu yan lokatai da suka wuce shi shugaban sojojin Nigeria Tukur Yusuf brutai yasha fitowa yace sun murkushe yan kungiyar boko haram a Nigeria Wanda mu da ta addancin yafi shafar bangaren mu muna jinsa munsan ba haka bane amma bamu taba fitowa mun karyata shi ba.
Sanata Ali Ndume yace yana kira ga shugaban sojojin Nigeria Tukur Yusuf brutai da ya janye wancan kalamai nasa Na zargin wasu sojojin Nigeria da hada baki da wasu yan siyasar kasar nan da yunkurin shirya juyin mulki a boye, domin shi kansa yasan wannan lafazin nasa ba gaskiya bane yayi ne kawai don ya wanke kansa da kuma yaudarar shugaban kasar Nigeria muhammadu Buhari don karya kai ga fahimtar cewa sun Gaza ya canza su da wasu, inji sanata Ali Ndume.