An jaddada tare da shawartar al’umma cewa, lokacin zaman zuru na jiran jami’an tsaro su kawo dauki a duk lokacin da ‘yan ta’adda suka kawo hari fa ya wuce, kuma Ya kamata kowa Ya yarda da hakan.

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari yayi wannan jan hankali a jawabin da ya gabatar wajen bude cibiyar sadarwa ta hada kan jami’an tsaro dake aiki a wannan jiha.

Gwamnan ya bayyana cewa duba da yawan al’ummar wannan jiha da kuma yawan jami’an tsaron dake akwai, hakika daukar matakan kare kai, musamman na kan ta farga, ya zama wajibi a gare mu baki daya.

Ya kara da cewa, ‘yan ta’adda suna amfani da sanin cewa bamu da wani shiri na hana su shiga garuruwan mu ballantana na tunkarar su idan sun shigo. Sai ya bada shawarar cewa jama’a su kirkiri hanyoyi da dabarun da duk za su iya domin kare kawunan su, Allah barshi su jami’an suyi abinda yayi saura.

A jawabin shi na maraba, Mai ba Gwamna Shawara a kan harkokin tsaro Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina ya bayyana cewa an kafa wannan cibiyar ne domin tabbatar da dukkan hukumomin tsaro suna samun bayanai bai daya kan lamarin tsaron wannan jiha. Ya kara da cewa, abin jin dadi ne kasantuwar wannan cibiyar itace ta farko a kasar nan, sannan kuma abin alfahari ne kwarai kasantuwar cewa fasahar da akayi amfani da ita ma ta gida ce domin kwararrun da suka hada manhajar da za ayi amfani da ita a wannan cibiya ‘yan jihar Katsina ne da sukayi karatun su kuma a jami’o’in dake nan Katsina.

Tun farko a nashi jawabin, wakilin kungiyar masu ruwa da tsaki kan tsaro ta jiha, Farfesa Bashir Kurfi ya jinjina wa Gwamna Aminu Bello Masari bisa ga irin goyon baya da hadin kai da yake ba wannan kungiya a cikin fadi tashin da take yi wajen bada gudummawa domin ganin an murkushe ta’addanci a wannan jiha.

Shugaban rundunar ‘yan sanda ta jiha, Kwamishina Sanusi Buba, shi ma ya bayyana jin dadi da godiyar jami’an tsaro ga Gwamnatin Jiha karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari a kan yadda yake tsaye a ko da yaushe wajen biyan duk bukatun da jami’an tsaron suke zuwa dasu. Ya kuma tabbatar da cewa wannan matsaya ta Gwamna Masari, ba karamin matsayi gare ta ba a kan duk nasarorin da suke samu a yaki da ta’addanci da kuma sauran laifuffuka a wannan jiha.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here