Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa lokacin bidar wanda za a dora ma laifin matsalar tsaro a kasar nan, musamman yankin arewa maso yamma, ya wuce. Abinda ke gaban mu yanzu shi ne hanya ko hanyoyin da za mubi don shawo kan wannan kalubale da ya ishi kowa kuma yaki ci yaki cinyewa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yau a Sokoto da kuma Abuja yayin da ya jagoranci tawagar kungiyar Gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma zuwa jaje da kuma ta’aziyyar wadanda suka rasa rayukan su a hannun ‘yan ta’adda a jihar Sokoton, wanda suka hada da mutane ashirin da ukku da ‘yan ta’adda suka banka ma wuta a cikin wata motar bas da suke tafiya a ciki.

A fadar Gwamnatin Jihar Sokoto, a madadin kungiyar Gwamnonin, ya mika sakon ta’aziyya ga Gwamnati da kuma al’ummar jihar bisa wadannan ibtila’o’i da ake ta fama dasu. Yayi addu’ar Allah Ya gafartawa wadanda suka rayukan su kuma Yaba iyalai da sauran dangi hakurin jure wadannan rashe rashe.

Gwamna Masari wanda yake tare da Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, sun mika gudummawa ta Naira Miliyan Hamsin a madadin kungiyar Gwamnonin domin tallafa ma iyalan wadanda wannan ibtila’i ya shafa.

Da yake maida jawabi, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana godiyar gwamnati da al’ummar jihar Sokoto bisa wannan karamci na yan’uwantaka da zumunci da aka nuna masu. Ya kuma roki Allah Ya yaye mana wannan masifa.

A Abuja kuwa, gidan tsohon Gwamnan Jihar kuma Sanata a yanzu, Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko, bayan isar da sakon ta’aziyya, Alhaji Aminu Bello Masari ya kara jaddada kiran shi, na al’umma su tashi tsaye su kare kawunan su daga wadannan ‘yan ta’adda.

Gwamnan ya kara da cewa a matsayin su na shuwagabanni, dole su kalli juna su gaya ma kawunan su gaskiya. Kowa ya san jami’an tsaron da akayi ma zuru su kare kasa basu da yawan da za su iya gudanar da wannan aiki yadda ya kamata, to ta wane dalili za ace wa al’umma su zauna zaman jiran samun kariya daga gare su ba tare su ma al’ummar sun yunkura ba.

A ta bakin Gwamnan, Mutane suyi zaune kurum, zaman jiran azo ayi masu ta’adi, ba tare da wani yunkurin kare kansu ba, hakika ya saba ma shari’a kuma ya saba ma hankali. Shi yasa musulunci yace duk wanda aka kashe wajen kare rayuwar shi, mutuncin shi ko dukiyar shi to yayi shahada.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa wajibi ne a kwato wannan daji daga hannun ‘yan ta’adda idan har za a kawo karshen wannan matsala. Amfani da Kimiyya da kuma kididdiga ta mazauna cikin dajin na kan gaba wajen samun nasarar hakan. Yace wannan shi ne salon da sukayi amfani dashi a kan dajin Falgore har suka samu cin dunun matsalar da taso tasowa cikin shi.

A nashi bangaren, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya mika godiyar su ga wannan kungiya ta Gwamnoni bisa wannan karramawa da akayi masu, wadda ta fito da dankon zumunci dake tsakanin al’ummomin jihohin. Ya kuma yi amfani da wannan dama domin yin kira ga Shuwagabanni da a aje maganar siyasa gefe guda, a tunkari wannan lamari ka’in da na’in domin kawo karshen shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here