Farfesa ilimin ƙwaƙwalwa, Farfesa Taiwo Sheikh ya ce ɓangaren likitocin ƙwaƙwalwa shi ne ya fi samun naƙasu a ɓangaren ƙarancin likitoci da ke faruwa a Nijeriya.

Sheikh, wanda shine tsohon Shugaban Ƙungiyar masu Ilimin Ƙwaƙwalwa, ya baiyana hakan ne a wata tattaunawa da Kamfanin Daillancin Labarai NAN a yau Alhamis a Legas.

A cewar sa, ɓangaren ƙwaƙwalwa shi ne ya fi ƙarancin ma’aikata a fannin lafiya sama da sauran fannoni.

Ya ce a na ƙarancin likitoci da sauran ma’aikatan lafiya a ɓangaren ƙwaƙwalwa.

Ya ƙara da cewa a kowanne likitocin ƙwaƙwalwa kwararru a Nijeriya, uku sun gudu ƙasashen waje su na aiki a can.

Sheikh, wanda Malami ne a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, ya nuna damuwa cewa ƙasar nan na da halin da za ta iya horas da likitocin ƙwaƙwalwa, amma ta kasa riƙe su.

Ya nuna cewa samun ilimin ƙwaƙwalwa biza ne a kan kan sa sabo da ma’aikatun lafiya a kasashen waje kullum cikin neman masu irin wannan ilimin su ke.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here