Advert
Home Sashen Hausa LAYIN DOGO DAGA KATSINA ZUWA MARADI HANYA CE TA BUNKASA TATTALIN ARZIKIN...

LAYIN DOGO DAGA KATSINA ZUWA MARADI HANYA CE TA BUNKASA TATTALIN ARZIKIN AL’UMMA….Inji Attahiru bala Usman.

 

Fassara daga jaridar thisday.

@ abdurahaman Aliyu

Attahiru Bala Usman, kwarare a fannin muhalli, ya ba da tabbacin cewa aikin layin dogo daga Kano zuwa Maradi da gwamnatin tarayya ke yi yana da fa’idodin yaduwar tattalin arziki ga al’ummomin da ke yankin dana tattalin arzikin Nijeriya baki ɗaya a matsayin ta na dunkulallar ƙasa.

Mista Usman, Wanda yake Manajan Darakta na kamfanin Allott Consulting Nigeria Limited, kamfanin da ke gudanar da kimanta tasirin muhalli da zamantakewa na aikin layin dogo na Kano-Maradi, ya bayyana hakan yayin wani aikin tantance wuraren da za a ajiye kayan aiki don kula da hanyoyin aikin jirgin.

Usman ya ce “kimanta tasirin muhalli da zamantakewa al’umma zai tabbatar da ci gaba mai dorewa wanda zai inganta rayuwar mutanen dake yankin a yanzu da kuma wadanda za su zo nan gaba ba tare da aikin yayi illa ga muhallin da yanayin zamantakewar mutane ba”. in ji Usman.

Babban layin dogo mai tsawon kilomita 284, za a samar mai tashoshi 15, da za a rika amfani da su. Jirgin zai bi ta kusa da garuruwa da kauyukan wadannan yankuna. Kano-Dambatta-Kazaure-Daura-Mashi-katsina-Jibiya-Maradi.

Tashoshin 15 sun kunshi manyan tashoshi guda biyu a Kano da Katsina, matsakaitattun tashoshi uku a Kazaure da Daura da Jibiya, kananan tashoshi uku a Shargalle, da Dambatta da Mashi, tare da sauran tashoshin da sauran matsakaitan tashoshi da suka hada da Kunya Dube, Muduru, Daddara, Anoal Mata da Maradi.

Usman ya bayyana cewa kammala aikin layin dogo daga Kano zuwa Maradi zai saukaka zirga-zirgar jama’a, zai bunkasa ci gaban tattalin arzikin noma, masana’antu a gefen hanya tare da rage tsadar kayan masarufi.

Da yake nuna mahimmancin aikin ga al’ummomin yankin da tattalin arzikin Nijeriya, ya ce duk ƙa’idojin muhalli na duniya da a ƙasa da aka gindaya ana tsammanin ɗan kwangila Mota-Engil Nigeria Limited zai bi su sau da kafa.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Alleged Defamation: Gov. Masari demands N10bn, apology from journalists

Gov. Aminu Masari of Katsina State has demanded the payment of N10 billion as damages from Mr. Emmanuel Ogbeche and Mr. Ochaika Ugwu, Chairman...

Biliyan Ɗari shida da Miliyan ɗari biyu da Hamsin, Tallafi daga Gwamnatin Tarayya domin ɓunƙasa Karkara da gandun Daji a jihar Katsina…..

Biliyan Ɗari shida da Miliyan ɗari biyu da Hamsin, Tallafi daga Gwamnatin Tarayya domin ɓunƙasa Karkara da gandun Daji a jihar Katsina..... A ranar Alhamis...

DIRECTOR-GENERAL INAUGURATES NYSC MEGA PRINTING PRESS

NYSC Director-General, Major General Shuaibu lbrahim today inaugurated the NYSC Mega Printing Press in Kaduna. He said the project, which was conceived almost a decade...

Shugaba Buhari Ya Miƙa Ta’aziyyarsa Ga Iyayen Hanifa, Yarinyar Da Aka Kashe A Kano.

Daga Zaharaddeen Gandu Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina wa 'yan sandan Jihar Kano game da gano wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar mai...